YAUNE RANAN DA ZAN BAYYANA KOMAI AKANKI
YouTube 43
Zuciyarkita zama takarda, tawa ta zama bir in rubata
miki shafin kauna Kizama kofa na Zano makulli, mu
hadu mu bude kofar soyayyyar lambun zuciyata! Na
kasa tsaye na
kasa zaune a lokacin da na fara ganin ki a cikin taro ,
kin fita daban kaman wata daren sha biyar!
Ya madarar zuciyata, ki zamo ciminti in zamo bulo
mu gina gidan
Quana a filin soyayya.Watau yau da na tashi, sai na ga
rana ta taso ta haske nan din nan amma duk haskenta
ba kai hasken fuskar
da haske zuciyata,domin ni a zuciyata Hasken fuskar
abun quana ta yafi duk hasken raina Ki zama petur na
zama inji mu hadu
mutaa da lantarkin qaunaya shiba ta na baki filin
zuciyata ki shuka aduk wani lungun da sako bushiyar
so a kauna don mu sami
inuwar da zamu zaunamuyi soyayya.
Kece madubi abar dubawata duk safiya, kin zamo min
tamkar fetur a mota, rayuwata bake
tamkr lami ce ya rabin raina
Ke ce makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na
sha za ta
haska ka zuciyata ta yi fari.
Rayuwata babu ke tamkar wayar da chaji ce, kuma
babu layi, a mace ba amfani.Kunne ya kur mance
saboda rashin jin kallamen quanar ki kullum, baki ya
daina magana dai
dai saboda rashin begen zumar rayuwata kullum.Ta
tsagwaron zallar tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona
zai makance saboda
rashinganinki a yau da kullumYa gangariyar madarar
zumar da batada gauraye, ya tauraruwa a cikin jinsin
taurari mai haske
zuciyar masoyinta. Idona ya bude ya ga haske irin na
walkiya don ya gan ki. Ziciyata na shan lagwadar
zuma da madarar kaunaIdon
basira lafazin rayuwata
Alfijirna quana ya keto, tsuntsayen soyayya sun tashi
su na
yayo a sararin samaniyar zuciyata Ya fankar da ke
juya zuciyata, zan zamo kwale kwale
ki shigo bu haukan kogin so, in zamo katifa ki zamo
gado a cikin dakin kauna.Hadarin begen ki ya hado,
guguwar sonki ta taso, sai
ruwa mai karfi ake yi na kaunar ki afilin
zuciyata.Gaisuwa daga kamfanin so, harabar
kauna,gida mai lambar zuciyata layin begen ki,
zuwaga rabin rayuwata.ya zare da allurar da ta dinken
zuciya ta, bazan taba daina sonki ba har sai wutar
lantarki ta zauna a
nijeriya. ya majaujawar zuciya ta, zan zama guga ki
zama igiya mu hadu a jefa mu cikin
rijiyar soyayya. Ya tsokar zuciya ta, zan so ace ki
zama furain zama nono mu hadu a kwaryar
soyayya.Ya sahiba ta ki zama
fukafikin dama in zama na hagu mu hadu mu ta da
tsuntsun soyayya.Ya masoyiyata ki zamo bishiya in
zamo ruwan da zai ratsa ta kasar so ba dan kome ba
sai dan in shayar
da ke.Ya masoyiyata, ki zamo hanta
inzamo jini, muga mai raba mu. Ludayin kaunar ki
ya mamaye min kokon zuciyata.Ya
masoyiyata ki zamo mai in zamo albasa mu hadu mu
soye juna.'.ya masoyiyata, ki zama candir in zamo
ashana, ki zamo itace in zamo makamashi mu hadu
mu hura wutar so, domin mu mutafasa tukunyar
kauna Kixama aruma naxama Sadauki mu hadu mu
yaki duk wani makiyin soyayyan mu daga naku baban
soyayya namalika
Comments
Post a Comment