KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA
KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA
GA
MASOYA
Idan kana tare da budurwa masoyiyarka, ya kasance
kanayi
mata kalamai masu dadi na jan hankali, wadanda zasu
dinga
faranta mata rai.
KAMAR HAKA
Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga
wacce
tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba
sai
ke masoyiyata
So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina
Kinfita daban a cikin mata, duk lokacin da na kallleki, sai
naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke
Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a
zuciyata
sai ke kadai
Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da
soyayyarki tagaskiya a gareni
Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki,
dan
haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba
masoyiyata
Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan
buqata, ko kinsan kece abu na farko da nike roqo samu!
Yanayin sanyi kan sa mutum ya takura, tare da lullu6a da
qaton mayafi amma ni duk sanyin da ake idan na tunaki
sai
naji tamkar yanayin zafi
Kamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma
tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina,
idan
na kalleki sai nayi farin ciki, idan naji tattausan muryarki,
sai
nishadi da walwala tare da annashuwa gami da farin ciki
su
mamaye zuciyata
Abokina ahakan zaka bi don sace zuciyar masoyiyarka
cikin
Allah y saka da Alkhairi naji dadin wannan kalaman
ReplyDeleteAllah y saka da Alkhairi naji dadin wannan kalaman
ReplyDeleteMuna godiya
ReplyDelete