RAYUWARMASOYA





Haske kan bayyana a dausayin zuciya a yayin da duhu ke
gaggawar
ficewa daga gare ta ba tare da ba ta lokaci ba Kafin
zuciya ta kafa tutar
samun nasarar cafke ragamar son wanda take so, za ka
same ta ne
tsundum cikin duhu mai tsanani sakamakon rashin
samun mai yayyafa mata feshin sinadarin so a gonar
ruhi. Ruhin dan-adam yana kasancewa ne cikin
wani irin yanayi na kwadayin samun mai kula
da shi a kowanne lokaci, wannan dalilin ne ya sa
zuciya ke tsananin son duk mai kyautata mata
da kuma kin duk mai takura mata
Kasancewar zuciya ita ce
tubalin ruhi sannan kuma na'urar dake kimtsa soye-
soyen ruhi, sannan kuma ma'adanar sirri, tana
kasancewa ne a cikin wani irin yanayi mai hasken
gaske da zarar ruhi ya sami abin da yake
muradi Tsananin hasken zuciya yana tasiri matuka
dan kuwa har fuska tana iya bayyanawa da zarar
ka ga wadda ke cikin shaukin so nan take za ka
iya ganewa.Duban masoya  a lokacin da
masoya biyu suka
kasance tare akwai wani irin satar kallo da masoya
ke aiwatarwa a tsakaninsu, kallo ne mai
girgiza zuciya har sai zuciya ta kakkabar da
duk wata damuwa da ta makale a jikinta. Hakika
kallon yakan sanyaya
zuciya matukar
sanyayawa musamman
idan an cakuda kallon da kalaman so masu gigita
wanda aka yi dominsa.A lokacin ne masoya za su ji
tamkar su kadai ne a duniya saboda tsananin
farin ciki da ya dabaibaye
zuciyarsu, gami da tsananin haske tamkar
farin zinare wanda aka ajiye shi a hasken farin
wata Hasken zuciyar masoya a irin wannan
yanayi wa ne hasken walkiya, domin ita
walkiya haskawa daya
take yi ta bace, amma zuciyar masoya kuwa
hasken zai kasance zaunanne a ruhi tsawon
zamani. Mhm! Soyayya hasken rayuwa, rashin
soyayya kuwa kuncin rayuwa Shin wai ma a
rayuwa akwai abin da ya fi soyayya dadi kuwa
Amma fa soyayyar da aka kafa gininta da
tubalin gaskiya ne kadai hakan ke faruwa Amma
ka ga soyayyar da aka gina ta da tubalin karya
kuwa sunanta rusasshiya, sannan kuma ba ta haifar
da komai sai damuwa da kunci da kuma shigar da
masu yin ta cikin halin ha'ula'i. Hasken so na
gaskiya shi ne fitilar dake haskaka zuciya, hasken
zuciya kuwa hasken rayuwa ne.

Comments

Popular posts from this blog

KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA