DALILAN DA YASA NA KORI RAHAMA SADAU




shugaba kungiyar wakan fina-finan Hausa na shiyya
Arewa, guda cikin mawakan da suka fara waka a
masana’antar shirya finafinan Hausa, shahararren
mawakin da ya rere wakar Sangaya Sangandale da
sauran wakokin da har yanzu taurauwar su ke
haskawa a tsakanin masu sha’awar fina-finan Hausa.
A tattaunawarsa da wakilinmu Sharfuddeen Baba a
Kano, Musbahu Ahmad ya yi tsokaci kan halin da
wakoki da mawaka suke ciki a yanzu, sannan kuma ya
bayyana dalilansu na kafa Kungiyar mawakan irin ta
farko Ga dai yadda tattaunawar ta kasance Bari mu
fara jin wanda muke tare dashi? Alhamdulillahi ni
sunana Musbahu M Ahmad Fadawa mai karatu
takaitaccen tarihin rayuwar ka? An haifeni a unguwar
Gwammaja dake Karamar Hukumar Dala a Jihar
Kano, nayi karatun firamare da sakandire duk anan
Kano, sannan nayi Tahfiz Alqur’an a Jihar Bauchi, sai
kuma karin ilimi da naje Kasar Maleshiya inda na
karanta International House Ko ya Musbahu ya tsinci
kansa a harkar
waka Ita harkar wakoki kasan komai yana da lokaci
hakan Allah ya yi muka wayi gari muka ganmu mun
tsinci kanmu acikinta tsundum, kasancewar ina da
sha’awa a cikin
waka. Mun fara waka a kamfanin Sarauniya fims dake
Gwammaja, dalilin zuwan da muke muna karbar fina-
finai muna kallo, wannan ta bamu dama muka fara
tattaunawa dashi daraktan kamfanin Aminu Mohd
Sabo, Allah cikin ikonsa aka fara jarraba mu, muka
samu
nasara na fara da fim din Allura da zare muka yi masu
wakoki, har kuma zuwa lokacin dana yi masu wakar
Sangaya wannan waka ta shahara kwarai a wannan
lokacin ni ne nayi wannan waka. Kasancewar muryar
Musbahu M. Ahmad sananniya ce a zukatan jama’a,
shin ko za’a iya tunawa masu karatu wasu daga cikin
wakokin da aka fara? Kafin Sangaya nayi wata waka a
fim din
Allura da zare wadda mu biyu muka yi wannan waka
ni da Mudassiru kasim shima sa’ana ne tare muka
fara yin wakokin fina- finan Hausa, sai kuma wakar
cikin Allura da Zare, sai wakar Na Gangaro,
Samodara, Adali a fim din Tattabara, sai kuma
Dawayya, Sangandali, Sanafahana da kuma irinsu
Kakaki na Koshuwa duk wakoki ne irin na gargajiya
duk ni ne na wallafa wadannan wakoki.
Da ka ambaci Sanafahana acikin wakar kamar a Nijar
akayi wakar, shin gaskiya ne can din akayi wakar? Ni
anan nayi wakar acikin studio amma wadanda suka
sakata cikin fim sune suka yi tattaki har kasar Nijar
kasancewar labarin ya
nuna haka, ni kuma dana tashi fitar da album din
wakar munyi amfani da wata al’ada mun tafi kan
ruwa, kamar yadda kowa yaga an sa
mata sunyi shigar Al’adar Hausa, yawancin abubuwan
da kaga ni cikin faifan Bidiyo dole sai anje ire-iren
wadanan wurare, amma ita wakar a studio aka yita.
kasancewarka guda cikin wadanda suka fara rera
waka a masana’antar shirya fina-finan kannywood ko
ya zaka kwatanta wakoki ada da kuma yanzu?
A baya wakoki basu da yawa kamar yanzu haka kuma
sakonnin ma suna tafiya dai dai da irin wancan
zamanin haka na yanzu ma suke tafiya dai dai da irin
wannan zamani,
duk da samun sauye sauye da akayi, ba sako kadai
ake aikawa da wakar ba, akwai yanayin kida akwai
yanayin murya da na’ura mai kwakwalwa ke gyarawa,
duk wadanan abubuwa ana kallonsu, sannan kuma
wakokin
sun banbanta, zaka ga abaya sakon kawai ake son
isarwa, amma yanzu an fadada abubwa zuwa tallace
tallace na haja, wakokin siyasa da Sarauta, saboda
haka duk sai suka taru a cikin harkar waka. Wanann
tasa ba irin sakonnin kadai ake ji ba. Da bamu da
yawa mawakan a lokacin da wakokin ke da tasiri duka
duka mu bakwai ne mawakan a wancan
lokacinlWadanda suka fi shahara a wancan lokacin
mu uku ne kadai, daga baya mutun biyu suka
karu aka kara samun wasu karin, duk zaka iya ji
wakokin kowane mawaki a wancan lokacin, yanzu
idan kace wakokin mawakan baki daya zakaji sai ka
shafe mako biyu baka gama jiba. Wannan tasa yanzu
ba zaka ji sakonnin kamar yadda aka saba jinsu a
baya ba, zamani ya juyasu ana aro al’adu, wata wakar
ma ta indiya ce za’a dauka da Karin da kidan a
fassara, wata ta larbaci ce
sabanin mu ada sai munyi nutso cikin al’adun
Bahaushe na gargajiya, lokacin dana ke fada maka
cewa mawakan mu bakwai ne, to yanzu a
matsayina na shugaban mawakan shiyyar Arewa da
muka tara mambobinmu tun lokacin da aka bamu
rikon kwarya, a gabana
abinda muka samu mawaka da suka yi rijista da
wannnan kungiya mutum 280 ne, kaga zai yi wuya ka
kwakwanta da yadda tsarin yake a baya. Dole a samu
canji tunani, ra’ayi, Al’adu, Ilimi da kuma wayewa ta
zamani fiye da ta da. Kasancewar ka shugaban
Kungiyar mawakan
shiyyar Arewacin Kasarnan, wane mataki ku ka dauka
domin ganin an daidaita tafiyar ‘ya’yan wannan
Kungiya domin kare kimarku?
Alhamdulillah daga cikin dalilan da yasa muka kafa
wannan kungiya shi ne domin saita harkar wakar ta
zama tana kan tsari, musamman rubutun ita Kanta
wakar, sai
kuma ci gaban da za'a samu ta hanyar wakar. Sannan
kuma ya za’a yi mawaki ya kasance mai kima da
mutunci da daraja, kuma Alhamdulillahi mun samu
hadin kan
mambobinmu, wanda ko a shekarar data gabata mun
gudanar da taron karrama wasu mawaka tare da
manyan Kasa, taron da aka gudanar a babban dakin
taron fadar Gwamnatin Jihar Kano, wanda Gwamna
Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya halarci
wannan taro kuma shima an karrama
shi a wurin taron. Saboda haka yanzu muna da tsarin
tace
wakoki bakowace waka zaka saki kawai ta shiga cikin
al’umma ba, domin kaucewa batawa wani daga cikin
Al’ummar mu. Alhamdulillahi anyi zaben shugabancin
kungiyar a Jihar Kano inda aka bani rikon
kwaryar shugabancin kungiyar a matakin kasa, amma
anan Kano ni aka zaba domin shugabantar shiyyar
arewa, sai kuma Bili 0 shi ne sakatare, Muntari Kabara
a matsayin
ma’aji. Muna cikin inuwar Kungiyar masu shirya fina-
fina hausa ta MOPPAN. Kai ne shugaban Kungiyar
mawakan Arewacin Kasarnan kuma anji wata
badaqala data faru da sunan waka wadda Rahama
Sadau ta aikata, shin ko me zaka ce kan haka?
Gaskiya wakarta bata ja mana komai ba a tsarin mu
na mawakan Hausa, na farko adalcin da mutane da
suka yi mana ba’a taba danganta wannan al’amarin
da
mawakan Hausa ba, na farko ba wakar Hausa bace,
sannan ba Musulmi ba ne kuma bama dan Arewa
bane ya jagoranci wakar,
sanann ita akashin kanta Rahama Sadau ba mawakiya
bace, jaruma ce a fina-finan Hausa. Amma wannan
bai hana a tuntube mu ba Kungiyarmu na cikin
inuwarMOPPAN
wadda duk taron da za’a yi dani ake yi, ina cikin
mutum tara na farko da muka fara daga hannu don
nuna amincewar mu da korarta daga masana’antar
shirya fina-finai, damu aka rattaba hannu kan takardar
korarta. Kakarin da muke a wannan masana’anta shi
ne me za muyi a kyauta Al’adunmu da Addininmu,
duk abinda zai ci karo da Addininmu da Al’adunmu
gaskiya zamu yi rigima dashi Muna sanar da jama’a
cewar sana’a muke an sanmu da mutunci a garin nan¸
don haka ba zamu yarda wani bako ya tsallako ba da
wata Al’ada wanda shima idan kaje nasu garin ba
Al’adarsa bace, saboda wata wayewa ya ja mana zagi
ya barmu ana kallon mu mutanen banza, idan ka zagi
Musbahu a kalla sama da mutum dubu ne a garin nan
zasu ji haushi, akwai Surikaina, Iyayena, Yayyena ,
Kannena, Surukan Kannena, saboda duk ina da alaka
dasu. Amma idan bako ya tsallako ya yi zagi sai a
gama maganganun ma wani bai jiba.
Musamman kila shi Al’adarsa ta halatta masa haka.
Wasu mutane sun shigo wannan masana’anta tayi
masu sutura tana binsu bashin mutunta ta, amma
kuma suna ja mata zagi, wadanda suka dabbaka
sana’ar a nan Kano basu ja mata zagi ba balle ace
masu ‘ya’yan kuka.
Gaskiya a layin da muka ja a halin yanzu ba zamu
kyale kowane mutum ya zo yaci gaba da ja mana zagi
ba balle mutumin da zai
tsallako, idan mutum ya ga ba zai iya kiyaye namu
dokokin ba ya koma Jiharsu ko garinsu ya kafa tasa
Masana’antar. Shin ko Musbahu na da shirin fitar da
wani sabon album yanzu? Na kan dade ban fitar da
album ba na kanyi shekara 4 - 5, album dina na
karshe yau
shekararsa biyu, amma duk da haka ina kokarin
sauyawa zuwa shekara daya ko biyu, na karshe shi ne
Laila, kafin shi akwai Ban kwana da Masoyi,
wadannan sune sabbin
album dina da suka fita wanda audio ne. banyi bidiyon
suba, shima dan Almajiri ana bina bashi ban yi
bidiyon sa ba har yanzu. Me yasa Musbahu Ahmad
baya rawa a lokacin da yake gudanar da wakokinsa Ni
da man haka na fara waka ta kuma haka
na san waka a wajena ni a nawa tunanin, a yanda na
fahimci waka irin wakoki na basa bukatar rawa,
bil’asali ma ni ban iya rawar
ba, ko da ma zanyi ba dole tayi min kyau ba tunda ka
ga ban iya ba bai kamata ma na fara ba. Ni ban dauki
rawa da cewar sai ka alakanta
ta da waka ba. Wakoki na sako ne wata Magana suke
aikawa, idan ana saurarar waka ta idan na kama rawa,
shin rawar za’a kalla ko sakon dana ke fatan isarwa
zai saurara
Bukata ta a saurari wakar ka fahimci sakon da ke
cikinta, sakon dana ke aikawa ya isa wurin da na ke
fata ko kuwa bai isa ba wannan shi ne babban buri na
a waka
Shin ko wa Musbahu ya fi gamsuwa da yin waka tare
da ita cikin masu amsa masa wakokinsa? Kwarai ina
da mutanen dana saba wakoki
dasu, wanda aka fi jin wakoki na dasu, amma ba wai
suna ajeye kawai don yimin amshi ba, suma zaman
kansu suke suna aikinsu, amma ni idan na fara rubuta
waka ina hangen muryar wacece zata dace da
wannan waka, idan ana daga murya sosai nasan
wadda zan
kirawo ta hau wannnan sautin, haka idan kasa kasa
nake yinta mai sanyi akwai wadda na tabbata zata fi
dacewa da wannan amshin. Shi yasa aka fi jina da
mace daya wajen yin
wakoki na.bKo mene sakonka na karshe ga ‘yan uwa
mawaka da sauran Al’umma?
Alhamdulillah sakona na farko ga mawaka ne aji
tsoron Allah a duk inda suke, duk abinda za kayi ka
tuna Ubangiji ka sani Duniya zuwanta kayi kuma barin
ta zaka yi, Kafin kai wani yazo ya tafi, idan takamarka
ka shahara wasu sun shahara kafin kai, kuma yadda
suka sauka haka kai ma wata rana dole ka sauka.
Wakar zagi ni ban yarda da ita ba, ka ci mutuncin
wani cikin waka don wani abin Duniya hakan ko kadan
bai dace ba, dole mutum ya kiyaye harshensa kwarai
da gaske, a kiyayi zarmewa da banbadanci cikin
wakoki, ka zama wani maroki ko wani abu daban.
Al’ummar gari kuma su ci gaba da bamu hadin kai
tare da yi mana Addu’a, sannan su taya mu duk
abinda su ka ga na gyara muna yi don gyaran wannan
masana’antar ce, idan muka tsaya akan gaskiya ya
kamata suma su tsaya akanta, abin mamaki sai wani
abu ya faru damu sai ayi caa ana zaginmu, idan kuma
ya faru muka dau mataki akashin kanmu sai kuma su
dai mutanen kaji suna cewa ba’ayi adalci ba, wanda
da an kyaleshi, sune zasu ci ga da tsine mana
albarka. Haka ta faru lokacin fim village aka dinga
dauko hotunan su Ali Nuhu da suka yi fim wanda ba
na Hausa bane, amma sai aka dinga yanko hotunan
su hade da mata ana nuna mana ana zagimu ana
tsine mana, yanzu wani abu ya faru da ‘yarmu Rahama
Sadau mun hukunta ta kafin ma Duniya tasani munce
bamu yarda da wannan ba, munja layi da wadannan
abubuwa, sai kuma ka ga wasu daidaiku sun shiga
social media suna kaimana harehare iri daban daban
cewa bamu hukunta wane da wane ba, kaga wannan
ba adalci bane, idan munyi shiru ku
zage mu, idan munyi hukunci kuma a
zagemu, saboda haka muna rokon mutane suyi mana
adalci, su kyale mu sana’ar mu ce mu yiwa kanm

Comments

Popular posts from this blog

KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA