AN BAYAR DA BELIN SHEKARAU



Wata babbar kotu a Kano ta bayar da belin tsohon gwamnan
jihar bayan da aka gurfanar da shi tare da wasu mutum biyu
bisa zargin halatta kudin haram.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau ne tare
da Tsohon Ministan harkokin waje Aminu Wali da kuma tsohon
Kwamishinan Ayyuka na Kano Mansur Ahmed.
Duka mutanen uku sun musanta tuhumce-tuhumce shida da
aka yi musu da suka hada da karbar kudi daga jam'iyyar PDP a
lokacin zaben 2015 duk da cewa sun san kudin ba ta
halattacciyar hanya suka fito ba.
Bayan sauraron duka bangarorin biyu, Mai shari'a Zainab
Abubakar Bagi ta babbar kotu da ke unguwar Gyadi-gyadi a
birnin Kano, ta bayar da belinsu a kan naira miliyan 100.
Wannan tuhuma na zuwa ne kwanaki kadan bayan hirar da
Malam Shekarau, wanda dan takarar shugaban kasa ne a PDP
ya yi da BBC, inda ya caccaki gwamnatin Shugaba
Muhammadu Buhari.
Magoya bayansa sun ce siyasa ce ta sa aka kama shi, amma
gwamnatin ta sha musanta zargin hakon 'yan adawa a shirinta
na yaki da cin hanci da rashawa.
Buhari bai iya mulki ba — Shekarau
Ba Kwankwaso ne ya kore ni daga APC ba - Shekarau
PDP ta zargi APC da 'murkushe abokan hamayyar siyasa'
Me ake tuhumarsu a kai?
Hukumar EFCC ta tuhumi jiga-jigan na jam'iyyar adawa da
aikata laifuka shida da suka shafi halatta kudin haram da hada
baki, lamarin da dukkansu suka musanta.
Karbar kudi naira miliyan 950 daga uwar jam'iyyar PDP ta
kasa
Sun san cewa kudin bai fito ta halattacciyar hanya ba -
halatta kudin haram
Sun karbi kudin duk da suna da masaniya sun fito ne daga
Tsohowar Ministar Mai Diezani Alison-Madueke
Ana tuhumar Ibrahim Shekarau da Aminu Wali da ajiye
kudin a wurinsu
Sannan suka raba kudin
Bayanan da mutanen suka yi shi ne cewa an raba kudin ne
domin gudanar da ayyukan zabe na jam'iyyar PDP mai mulki a
wancan lokaci kamar yadda uwar jam'iyyar ta nemi a yi.
Sun ce an raba kudin ne ga shugabannin jam'iyya a dukkan
matakan jihar kamar yadda kowacce jam'iyya ta ke yi.
Wannan ya sa wasu ke tambayar cewa ko EFCC za ta bi
dukkan shugabannin PDP a kananan hukumomin Kano 44 da
suka karbi kudin domin kamo su.
Wakilin BBC a Kano, Ibrahim Isa, ya ce kotun ta cika makil da
magoya baya 'yan siyasar, kuma sai da jami'an tsaro suka yi
harbi sama da harba hayaki mai sa hawaye sannan aka
tarwatsa jama'ar da suka taru a wajen kotun lokacin da za a
fita su.
Ya kara da cewa mutanen uku sun isa kotun cikin shigar
kamala kamar yadda suka saba yi, kuma babu wata alamar
damuwa a tare da su.
Lauyoyin da ke kare bangarorin biyu sun kai ruwa-rana kafin
daga bisani lauyan wadanda ake kara ya nemi belinsu.
Kuma ba tare da wata jayayya ba lauyan EFCC ya amince
amma ya nemi a sauya sharudda masu karfi.
Bayan hutun dan lokaci, Mai Shari'a Zainab ta dawo inda ta
bayar da belinsu kan kudi naira miliyan 100 da kuma samar da
mutum uku da za su tsaya musu.
Daya daga cikin mutanen wajibi ne ya kasance ma'aikaci da ya
kai mukamin darakta da kuma wanda ya mallaki babbar kadara
a yankin da ke karkashin ikon kotun.
Sai a ranar 26 ga watan Yuni za a ci gaba da shari'ar.

Comments

Popular posts from this blog

KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA