ABUBUWAN DA MASOYA BA SA SO ALOKACIN DA SU KE HIRA



Da yawan masoya na ƙorafi kan masoyansu duk da cewa
matsalolin na da yawa amma zan ɗan yi duba akan
wasu
daga ciki.
Matsalar farko ita ce, wani namijin ya tsani jira yayin da
ya je
zance wajen budurwarsa, wannan daɗewar tana saka
masa
ƙuna cikin zuciya koda kuwa ya tawo tare da farin ciki;
wasu
mazan suna kasa jurewa sai su kiran hakan da wulaƙanci.
Yana da kyau ‘yan uwana mata da su yi haƙuri, su rage
yawan jinkiri a lokacin da masoyansu suka zo domin
faranta
musu, don wata ta san zai zo, maimakon ta shirya tun
kafin
ya zo a a! Sai bayan ya zo zata fara shiryawa. Wata ma a
lokacin za ta shiga wanka, sai ya gama ɓata lokacinsa
idan
yana da wani uzirin nasa ma sai ya haƙura ala dole tunda
kin
ɓata masa lokacin da ya gama lissafa abubuwan da zai
yi a
wannan ranar. Sai dai kawai ya danne zuciyarsa ya nuna
miki
hakan babu damuwa saboda yana son ki.
Ita kuwa ta yi ta washe baki babu wadda yake so sama
da ke
kuma ba za ki canja ba. Ki sani a duk lokacin da ya samu
wadda ta fi ki iya soyayya da nuna kulawa barinki zai ya
koma wurinta. Ko kuma ku yi ta samun matsala da shi
saboda kina ƙona masa zuciya, koda a ce ba kya son sa
akwai hanyoyin da za ki bi domin ku rabu lafiya.
A wani ɓangaren kuma wata macen takan fito zance
tana
taunar cingam (chewing gum), wanda maza da yawa sun
tsani hakan, idan wani na son hakan, wani ba ya so, a
nawa
tunanin ma babu wanda zai so hakan, akan kanki ma
idan
kika yi tunani sosai za ki iya gane cewa matsayinki na ‘ya
mace me tarbiyya wadda ta taso cikin al’adar malam
Bahaushe yin hakan ba daidai ba ne.
Wani namijin daga wannan halin da ta nuna masa zai ji
soyayyarta ta fita a ransa koda kuwa akwai sauran son
da
yake mata, yakan kasa sanin yadda zai fito ya faɗa mata
matsalarta wanda ita a nata tunanin daidai ne.
Bari na daɗa hangawa a wani ɓangaren da yawan maza
ba
sa son suje zanje kuna hira kita ce masa (uhmm…), ko
kuma
(ina ji), shi ma hakan maza da yawa basa buƙatarsa shi
namiji yana so ki buɗe baki kiyi masa magana kar ki ce
‘wannan ai wannan zubar da aji ne’ ko kaɗan da yawan
matsaloli na soyayya akwai abunda in har kin yi su ba
zubda
aji ba ne.
Har ila yau su ma mazan, ya kama su fahimta cewar a
cikin
mata akwai waɗanda ba su da yawa daga halayenku.
Wata
macen bat a son maimaita zance kullum, ka zo zance
hirar
da za ka yi mata ta wancen zuwan da ka yi ne, yana da
kyau
kafin ka je zance ka tsara abinda za ka faɗa mata wanda
za
su sanyaya mata zuciya ya sa ta farin ciki ta tuna da kai
yayin
da ka koma gida.
Kar ka zo kai mata hiran Messi da Ronaldo ko
Manchester
da duk ma abinda ya shafi ƙwallo to mace ta tsane shi a
wajen zance, duk da dai wasu matan su ma ‘yan ƙwallon
ne
amma dai da yawan mata basa buƙatar irin wa ‘yan nan
hirar
yayin da suke tare da masoyan su, ko hirar biki ko ta fim
da
dai sauran su, sai a tsaya ayi tunanin hirar da ta shafi
masoyiyar ko masoyin wajen yaba halaye da kyawu da
kuma
yadda za a tsara rayuwa da sauransu, hakan shi yake
ƙara
ƙaunar juna tare da tuna juna a koda yaushe.

Comments

Popular posts from this blog

KALAMAN SOYAYYA MASU RATSA ZUCIYAR MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA

KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA GA MASOYA